Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce akwai wandanda ke daukan nauyin ruruta rikin makiyaya da Benue

- Atiku ya ce rashin fahimtar juna tsakanin manoma na kabila Tiv da makiyaya Fulani ce dalilin afkuwar rikice-rikicen

- Atiku ya ce zai kawo karshen rikice-rikicen muddin aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2018

Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takara a PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce rashin fahimtar juna ne ainihin dalilin da yasa ake samun rikici tsakanin manoma 'yan kabilan Tiv da fulani makiyaya.

Atiku ya yi wannan jawabin ne a jiya Lahadi yayin da ya ke magana da manema labarai a fadar mai martaba sarkin makurdi, Abu King Shuluwa lokacin da ya kai masa jiyarar bangirma.

Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

Atiku wanda shine ke rike da sarautar Zege Mule U Tiv wato shamakin kasar Tiv ya ce warware rikicin makiyaya da manoma a Benue abu ne mai sauki.

"Fulani da Tiv sun dade suna zaune lafiya. Na yi imanin wasu ne suke daukan nauyin jefa rashin jituwa tsakaninsu. A matsayina na Zege Mule U Tiv, na jagoranci zaman sulhu da yawa a baya," inji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce zai kawo karshen rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoman ta hanyar amfani da sabbin hanyoyi da su kafi dacewa.

Kazalika, Atiku ya ce zai goyi bayan duk dan takarar shugabancin kasa da jam'iyyar PDP ta tsayar muddin anyi adalci da gaskiya wajen zaben fidda gwanin da za'ayi a ranar 5 da 6 ga watan Okctoban 2018 a Rivers.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel