Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

A ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal ya isa sakatariyar jam’iyyar dake Abuja domin a tantance shi.

Tambuwal ya kasance a ofishin PDP da misalin karfe 10:43 na safe domin tantcewar wanda wata kwamiti karkakashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ke gudanarwa.

Da yake Magana a daidai lokacin da ya isa wajen, Tambuwal wanda ya kasance gwamnan jihar Sokoto yace Najeriya na bukatar a kafa cibiyoyin da zasu isar da sake fasalin tattalin arzikin kasa da kuma bunkasa ta.

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)
Source: Facebook

Gwamna Tambuwal wanda har yanzu yake cikin dakin tantancewar tare da sauran yantakarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar yace: “Akwai yiwuwar daukaka Najeriya kuma makomar a yanzu take.”

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)
Source: Facebook

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)
Source: Facebook

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ahmed Makarfi ya bayyana cewa shi zai yi nasara wajen samun tikitin Jam’iyyar PDP domin ya fi kowa cancanta.

KU KARANTA KUMA: 2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda da ya mallaka ga Atiku

Tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna yayi wannan jawabi ne a Jihar Kebbi lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman inda ya fadawa manyan PDP a Yankin cewa shi ne yake da abin da duk sauran ‘Yan takaran na PDP ba su da shi.

Sanata Ahmed Makarfi yace sauran ‘Yan takaran na PDP sun cancanta amma sai dai shi ne kurum ya iya rike Jam’iyyar adawar a lokacin da abubuwa su ka sukurkuce har ta kai PDP ta kawo inda ta ke a halin yanzu ake sha’awar ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel