Ya kamata Shugaban kasa ya rika yin shekara 6 a kan mulki - Robert Audu

Ya kamata Shugaban kasa ya rika yin shekara 6 a kan mulki - Robert Audu

Mun samu labari cewa Cif Robert Audu wanda tsohon Ma’aikaci ne a Fadar Shugaban kasa ya bayyana cewa ya kamata Shugaban kasa ya rika yin shekaru 6 ne a kan karagar mulki a maimakon 4 da ake yi domin a rage kashe kudi.

Ya kamata Shugaban kasa ya rika yin shekara 6 a kan mulki - Robert Audu

An nemi a rika zabe bayan shekaru 6 domin rage barna
Source: Depositphotos

Robert Audu wanda tsohon Sakataren din-din-din ne a Fadar Shugaban kasa yayi kira a sake duban tsarin shugabanci a Najeriya a maida tsawon wa’adin shugaban kasa zuwa shekaru 6 ya kuma nemi a fara hakan daga kan Shugaba Buhari.

Cif Robert Audu ya koka da irin makudan kudin da ake kashewa wajen yin zabe ganin yadda ake neman kashe kusan Naira Biliyan 400 domin gudanar da zaben 2019. A dalilin haka Roberts Audu yace a rika yin zaben bayan shekaru 6 a Najeriya.

KU KARANTA: Makarfi yace PDP za ta iya doke Buhari a zaben 2019

Tsohon Sakataren na din-din-din Robert Audu ya nemi a karkatar da rarar kudin da ake kashewa a zabe wajen wasu abubuwan na gina kasa. Mista Audu yana kira a dadawa Buhari shekaru 2 domin yayi har shekaru 6 yana mulki a maimakon 4.

Audu yace sun yi wannan kira a 2005 amma aka yi watsi da shi. A mulkin Jonathan ma dai an yi irin wannan kira amma ba a kai ga samun nasara ba. Wasu na neman ganin an maida wa’adin Shugaban kasa sau guda rak na tsawon shekaru 6.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel