Gwamna El-Rufai ya kammala shirin daukan sabbin malaman asibiti 3,059 a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya kammala shirin daukan sabbin malaman asibiti 3,059 a Kaduna

Hukumar kula da kananan asibitocin mazabu na jahar Kaduna inda ake karbar magani da karbar haihuwa ta samu izini daga gwamnatin jahar Kaduna da ta dauki sabbin malaman asibiti guda dubu uku da hamsin da tara, 3,0659.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan lafiya na jahar, Dakta Paul Manya Dogo ne ya sanar da haka a yayin wani taron manema labaru daya gudana a garin Kaduna, inda yace an dauki matakain ne don samun isassun ma’aikata da zasu yi aiki a kananan asibitoci dari biyu da hamsin da biyar (255) dake mazabun jahar.

KU KARANTA: Aikin ganganci: Jami’an hukumar Kwastam sun bindige wani matashi a Katsina

Paul Dogo ya bayyana cewa daga cikin manyan manufofi da muradun gwamnatin jahar Kaduna shine farfadowa tare da inganta harkar kiwon lafiya a jahar don amfanin al’ummarta, ya kara da cewa a yanzu haka gwamnati ta dauki likitoci ashirin da uku, 23, da zasu yi aiki a kananan hukumomin jahar.

A wani labarin kuma akalla muta dari da ashirin ne suka rasu a sakamakon haihuwa a asibitocin gwamnatin jahar Kaduna guda Talatin daga watab Janairun bana zuwa Yuni kamar yadda wani rahoton gwamnatin jahar ta bayyana.

Rahoton tace daga cikin matan da suka mutu akwai mata ashirin da suka mutu a asibitocin gwamnati guda goma sha biyu a yankin kudancin Kaduna, sai mata sittin da takwas a asibitoci 10 a yankin Kaduna ta tsakiya, da mata Talatin da biyar da suka rasu a yankin Arewacin jahar.

Bugu da karin rahoton ta yi kira ga gwamnati data gyara ma’ajiyan jini dake asibitocin jahar domin a dinga samun jinin da za’a kara ma mata masu haihuwa wanda rashinsa ke janyo mutuwar yawancin matan, haka zalika tayi kira da a gyara motocin daukan marasa lafiya da kuma samar da wutar lantarki domin ajiyan jini a na’urar mai sanyi.

A nasa jawabin, kwamishinan kiwon lafiya na jahar, Paul Dogo ya bayyana cewa gwamnatin jahar da na kananan hukumomi na aiki tukuru wajen magance matsalar rashin jini a asibitocin jahar, haka zalika batun matsalar rashin wuta a asibitocin na gab da zama tarihi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel