Ndume yayi kaca-kaca da Bukola Saraki da Dogara bayan sun koma PDP

Ndume yayi kaca-kaca da Bukola Saraki da Dogara bayan sun koma PDP

Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki watau Ali Ndume ya bayyana cewa Majalisa tayi kasa a gwiwa a karkashin jagorancin shugaban ta Bukola Saraki.

Ndume yayi kaca-kaca da Bukola Saraki da Dogara bayan sun koma PDP

Saraki da Dogara sun maida Majalisa gidan su – Sanata Ndume
Source: UGC

Sai dai Sanatan ya nyna cewa yanzu ya zama dole Bukola Saraki ya bar mukamin sa na Shugaban Majalisar Dattawa tun da ya sauya-sheka daga APC zuwa PDP. Ndume yace APC ce ke da rinjaye don haka ya kamata ta rike Majalisa.

Ali Ndume ya koka da yadda Saraki da Dogara su ka rufe Majalisun kasar a lokacin da ya zanta da manema labarai a Abuja. Jiya Sanatan na APC ya nunawa ‘Yan jarida cewa babu abin da zai hana a tsige Saraki a Majalisar Dattawan kasa.

KU KARANTA: Ba Shugaban kasa Buhari ke rike da Najeriya ba Inji Bukola Saraki

Ndume yace Saraki zai tsira ne kurum idan ‘Yan uwan sa su ka nuna cewa su na tare da shi inda ya kuma kalubalanci Saraki ya jarraba farin jinin sa a Majalisa. Sanatan yace ba dole sai an samu kaso 2 cikin 3 ne za a iye tunbuke Shugaba ba.

‘Dan Majalisar na Jihar Borno dai ya nuna cewa Majalisa ba tayi abin da ya dace gare ta ba a wannan karo inda ya daura laifin kan shugabannin ta wanda yace sun maida Majalisar kamar ta gidan su alhali shugabanci ne kurum su ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel