Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu

Majalisar tarayyar Najeriya; majalisar wakilai da ta dattijai, ta bayyana cewar ba zata dawo daga hutun da ta tafi a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, ba tare da bayyana ranar 9 ga watan Oktoba a matsayin ranar da suka matsar da dawowar ta su.

Wannan sanarwa na kunshe cikin sanarwar da magatakardar majalisa ya aike ga mambobin majalisar wakilai da ta dattijai a yau, Lahadi.

Ina mai sanar da dukkan ‘yan majalisar tarayya cewar dawowar majalisa daga hutun da ta tafi ya koma ranar 9 ga watan Oktoba sabanin ranar Talata, 25 ga watan Satumba da majalisar ta tsayar a baya. Daga ranar dawowar ya biyo bayan harkokin tantance masu son tsayawa takara da jam’iyyun siyasa ke yi.

Ana tsammanin dukkan mambobin majalisar tarayya zasu dawo bakin aiki da misalign karfe 10:00 na safiyar ranar 9 ga watan Oktoba,” kamar yadda yake kunshe cikin sanarwar.

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu

Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu
Source: Twitter

'Yan Najeriya sun dade suna guna-guni a kan tafiyar majalisa hutu sabanini su zauna domin cigaba da tattauna batutuwan da suka shafi kasa.

Sai dai a bangare guda, wasu na ganin shugabannin majalisar sun zabi rufe zaman majalisar ne don biyan bukatun kansu.

DUBA WANNAN: Tsohon hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC

Jim kadan bayan rufe majalisar ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya canja sheka daga APC zuwa PDP kafin cikin kwanakin baya-bayan nan shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bi sahun Saraki zuwa PDP.

Akwai fargabar cewar mambobin jam'iyyar APC dake da rinjaye a majalisun zasu tayar da kayar baya tare da yunkurin tsige shugabannin nasu da suka koma jam'iyyar adawa PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel