Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC

Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC

Mista Kassim Afegbua, tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Edo, lokacin da da Adams Oshiomhole ke gwamna, ya fita daga APC tare da dumbin magoya bayansa.

Kafin kasancewar sa kwamishina, Afegbua ya kasance mai bawa tsohon gwamna Oshiomhole shawara a kan yada labarai.

Afegbua da dumbin magoya bayansa sun canja sheka daga APC zuwa PDP, kuma shugaban jam'iyyar a jihar, Cif Dan Orbih, ya karbe su yau, Lahadi, a garin Okpella dake karamar hukumar Etsako ta gabas.

Tsohon hadimin na shugaban APC na kasa ya bayyana cewar ya koma tsohuwar jam'iyyarsa, PDP da ya bari na tsawon shekaru 8, saboda gazawar gwamnatin APC na kawowa jihar Edo cigaba na a zo a gani.

Hadimin Oshiomhole da dumbin magoya bayansa sun fita daga APC

Oshiomhole
Source: Depositphotos

Kazalika, Afegbua ya koka bisa rashin wutar lantarki, hanya mai kyau da cigaba a garinsa, Okpella.

Ya kara da cewar 'yan APC daga garinsa na fita daga jam'iyyar ne saboda ta gaza kawo masu aiyukan cigaba.

Afegbua ya ce jama'ar sa na da hujjar komawa PDP ko don irin tallafin da ta bayar ga jama'ar da annobar ambaliyar ruwa ta shafa.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP ta bayyana hujjojin lashe zaben jihar Osun, ta soki komawa zagaye na biyu

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarar gwamnati da wasu tsiraru suka mallaka ba bisa ka'ida ba ya samu sahalewar kotu domin kama Sanata Peter Nwaoboshi bisa tuhumar sa da karkatar da dukiyar jama'a da cin hanci.

Wata kotun majistare dake Wuse II ne karkashin jagorancin mai shari'a Akanni Olaide ta bawa kwamitin takardar izinin kama Sanata Nwaoboshi a ranar 18 ga wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel