Tuwa-na-mai-na: Kwankwaso ya kara fito da wasu surukkan sa 2 takara

Tuwa-na-mai-na: Kwankwaso ya kara fito da wasu surukkan sa 2 takara

- Kwankwaso ya kara fito da wasu surukkan sa 2 takara

- Ya basu fom din takarar majalisar wakillai ne

- Kawunan 'yan kwankwasiyya ya fara rabuwa

Kasa da kwana daya bayan jagoran darikar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fito da surukin sa, Abba Kabir fom din takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2019, ya kuma kara fito da wasu surukan nasa biyu.

Tuwa-na-mai-na: Kwankwaso ya kara fito da wasu surukkan sa 2 takara

Tuwa-na-mai-na: Kwankwaso ya kara fito da wasu surukkan sa 2 takara
Source: Twitter

KU KARANTA: Hukumar kididdiga ta fallasa yawan bashin da ake bin Najeriya

Kamar dai yadda muka samu, Sanatan da yanzu haka yake neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP ya fito ne da surukan nasa takarar kujerun majalisar tarayya a jihar ta Kano.

Legit.ng ta samu cewa surukan nasa sune Mukhtar Yerima da ya tsaida dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni sai kuma Nasiru Sule Garo wanda shi kuma ya tsaida mazabar Gwarzo/Kabo.

Sai dai mun samu cewa tuni wannan halin na tuwo-na-mai-na da tsohon gwamnan na Kano ya nuna ya fara kawo rabuwar kawuna a tsakanin mabiya darikar ta Kwankwasiya inda wasun su ke guna-gunin cewa hakan bai tace ba.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma suka gudanar da zaben gwamna a jihar ranar Asabar din da ta gabata ya fadi abun da ke ran sa jim kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta bayyana sakamakon zaben.

Gwamnan jihar wanda wa'adin sa zai kare nan da yan watanni, Rauf Aregbesola ya ce shi yayi zaton za suyi wa jam'iyyar adawa a jihar ta PDP kwaf daya ne a zaben ba sai an je zagaye na biyu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel