2019: Ba ni da wani zabi da ya wuce David Mark - Jonathan

2019: Ba ni da wani zabi da ya wuce David Mark - Jonathan

Mun samu cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana mafificin zabinsa cikin manema tajarar kujerar shugaban kasar nan da za su fafata a yayin babban zabe na 2019.

Jonathan yayin zayyana zabinsa cikin manema takarar kujerar shugaban kasar ya bayyana cewa, ba bu wani dan takara da zai iya hada kan al'ummar kasar nan wuri da face tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark.

Tsohon shugaban kasar yake cewa, David Mark shine kadai yake da cancanta gami da nagarta ta hangen nesa da zai iya fayyace tsakanin daidai da rashinsa wajen hada kan al'ummar kasar nan a 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, Jonathan ya bayyana hakan ne yayin da tsohon shugaban majalisar ya ziyarce shi har gidansa dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

2019: Ba ni da wani zabi da ya wuce David Mark - Jonathan

2019: Ba ni da wani zabi da ya wuce David Mark - Jonathan
Source: Depositphotos

Ya ci gaba da cewa, ba ya ga kalubale na gurbacewar tattalin arziki da kalubale na tsaro, shugaban kasar Najeriya na gaba zai kuma fuskanci babban kalubale na rashin hadin kan al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Ni ne dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC - Makarfi

Legit.ng ta fahimci cewa, Jonathan yayin kyautata zaton samun nasarar jam'iyyar PDP a babban zaben na 2019, ya kuma bayyana cewa ba bu mafificin dan takara da ya kamata al'ummar Najeriya su dankawa amanarsu a hannu face David Mark.

A nasa jawaban, Sanata Mark ya sha alwashin dawo da Najeriya kan turba ta daidai tare da fidda ita zuwa kan tudun tsira cikin shekaru biyu na farko a kan karagar mulkin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel