PDP ta fara guna guni kan jinkirin da INEC ta ke yi na sanar da sakamakon zabe

PDP ta fara guna guni kan jinkirin da INEC ta ke yi na sanar da sakamakon zabe

- Rikicin siyasa na ci gaba da ruruwa a jihar Osun a zaman jiran da ake yi na bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar

- PDP ta fara guna guni kan jinkirin da INEC take yi na sanar da sakamako

- Jam'iyyar ta kuma tayar da kura kan jami'in INEC da aka kama ya yaga sakamakon zabe

Jam'iyyar adawa ta PDP ta fara kumfarfakin baki dangane da jinkirin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na bayyana wanda ya samu nasarar zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala a jiya Asabar.

PDP ta bayyana hakane a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa wannan jikirin ba abu ne da ya kamata hukumar ta yi ba a wannan lokaci, musamman ganin yadda abubuwa ke kara dagulewa, biyo bayan cafke wani jami'in hukumar INEC da ya yaga sakamakon zaben wata karamar hukuma.

Jam'iyyar ta ce jinkirin jami'i mai karbar sakamako na hukumar INEC a jihar na bayyana dan takararta, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wannan ya lashe zaben, ba lamari bane da za ta zura idanuwa ba tare da ta tanka ba.

KARAN WANNAN: Zaben Osun 2018: Adadin yawan kuri'un da kowacce jam'iyya ta samu

Jami'in INEC da ya yaga sakamakon zaben wata karamar hukuma

Jami'in INEC da ya yaga sakamakon zaben wata karamar hukuma
Source: Original

"Kin bayyana dan takararmu Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasarar zaben gwamnan jihar Osun ya saba wa doka tunda dai an riga da an kammala gabatar da duk wasu takardu da bayanan da hukumar ta ke bukata," a cewar jam'iyyar.

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa jam'iyyar PDP ta tayar da kura bayan da aka kama wani jami'in hukumar INEC mai suna Alao Mutiu Kolawole, da laifin yaga sakamakon zaben karamar hukumar Ayedaade.

PDP ta ce an yi mata runton kuri'u 1000 daya, cikin kuri'u 10,836 da aka sanar a rumfar zabe, wanda ya saba da kuri'u 9,836 da aka sanar a shelkwatar hukumar da ke Osogbo. Zaben da aka kawo shelkwatar ya nuna cewa dan takarar APC Oyetola ya samu kuri'u 10, 861.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel