Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Amurka

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja zuwa kasar Amurka domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya.

Shugaban kasa ya tafi tare da uwargidansa, Aisha Buhari.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da hakan a jiya cewa shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a yau Lahadi.

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Amurka

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Amurka
Source: Twitter

Yace: "Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi New York gobe Lahadi domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya UNGA37 wanda aka kaddamar ranan 18 ga watan Satumba, 2018."

Taken taron gangamin na wannan shekaran shine: "Ganin cewa majalisar dinkin duniya ta amfani mutane gaba daya'.

Babban abinda Buhari zai yi a Amurka shine jawabinsa da zai gabatar ga taron gangamin ranan Talata, 25 ga watan Satumba 2018 inda zai jaddada matakin da Najeiya take dauke wajen samar da zaman lafiya da tsaro."

Kana ana sa ran zai bukaci taimakon kasashen duniya wajen yaki da rashawa, dawo da kudaden sata da kuma yaki da ta'addanci."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel