Jam'iyyar PDP da APC sun kai matakin karshe a zaben Gwamnan Osun

Jam'iyyar PDP da APC sun kai matakin karshe a zaben Gwamnan Osun

Yanzu haka dai Karamar Hukuma guda kadai ta rage a gane wanda zai lashe zaben sabon Jihar Osun. Wannan Karamar Hukuma dai ita ce Osogbo inda nan ne babban Birnin Jihar Osun kuma mai mafi yawan Jama’a a kaf Jihar.

Jam'iyyar PDP da APC sun kai matakin karshe a zaben Gwamnan Osun

Kuri'un Osogbo ake jira domin a gane wanda zai zama sabon Gwamnan Osun
Source: Original

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da zarar an samu cikakken sakamakon Garin Osogbo za a gane wanda zai zama sabon Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai an kawo sakamakon kananan Hukumomi 29 cikin 30 da ake da su.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC tana da kuri’u 224, 488 yayin da Jam’iyyar adawa na PDP ke da kuri’a 236, 784. Hakan na nufin PDP ta sha gaban APC da kuri’a 12, 000. Yanzu dai sakamakon Osogbo kurum ake sa rai ya fito.

KU KARANTA: Sakamakon zaben Jihar Osun sun nuna an sha gaban APC

Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe Kananan Hukumomi 11 kacal. ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas.

A Garin na Osogbo dai ana iya samun kuri’u fiye da 50, 000 wanda hakan ya sa PDP ta fara kukan murdiya tuni. Idan har APC ta kerewa Jam’iyyar PDP da kuri’a fiye da 12, 000 a nan, to za ta lashe zaben inda za ta cigaba da mulkin Jihar.

Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC mai mulki dai ne zai kara a karshe da Sanatan Osun ta yamma Ademola Adeleke. Iyola Omisore na Jam’iyyar adawa ta SDP kuma ya lashe kuri’un Garin Ife.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel