Har yanzu Jigon APC Tinubu ya ki dagawa Gwamna Ambode kafa

Har yanzu Jigon APC Tinubu ya ki dagawa Gwamna Ambode kafa

Mun ji cewa babban Jigon Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ki marawa Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode baya a zabe mai zuwa da za ayi. Majalisar GAC da ke ba Gwamna shawara dai ta ki dafawa Mai Girma Ambode.

Har yanzu Jigon APC Tinubu ya ki dagawa Gwamna Ambode kafa

Ambode zai fafata da Hamza da Sanwo-Olu wajen samun tikitin APC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Majalisar ta GAC wanda ita ce koli wajen duk wani mataki da za a dauka a siyasar Legas ta tashi zaman ta wannan makon inda ta nuna cewa dole ayi zaben kato-bayan-kato a Jam’iyyar APC a Legas.

Mutane 22 na Majalisar sun gana a Gidan tsohon Gwamna Bola Tinubu inda su kace dole ayi zaben ‘yar tinke wajen tsaida wanda zai zama ‘Dan takarar Gwamnan Legas. Hakan dai babbar barazane ce ga Gwamna ma-ci Ambode.

Idan har Jam’iyyar ta dauki wannan mataki, Gwamna Ambode zai kara ne da Babajide Sanwo-Olu da kuma Dr. Femi Hamzat. Ana tunanin cewa Bola Tinubu na tare da Babajide Sanwo-Owu wanda tsohon Kwamishinan Jihar ne a da.

KU KARANTA: Gwamna Ambode ya karyata rade-radin rikicin sa da Tinubu

Majalisar ta GAC ta kunshi Gwamna da sauran manyan Jam’iyya da kuma Jigogin manyan Yankuna na Jihar. Daga cikin wanda ke cikin wannan Majalisa akwai irin su Dr. Olorunfemi Bashorun da kuma Sanata Anthony Adefuye.

Sauran wadanda ke cikin wannan da’ira sun hada da; Tunde Samuel, Cif Adeyemi Ikuforiji, Alhaji Tajudeen Olusi da wani Cardinal James Odumbaku wanda duk sun nuna cewa dole APC tayi zaben fitar da gwani a mako mai zuwa a Legas.

Kwanakin kunji cewa Matar Gwamna Ambode watau Bolanle Patience Ambode ta je wajen taron yakin neman zaben APC a Osun inda tayi kokarin ganawa da Tinubu domin ceto kujerar Mijin ta a zaben 2019 amma sam abin ya ci tura.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel