Zaben Osun: An ji karar harbin bindiga a wurin tattara sakamako, an kasa karasawa wurin

Zaben Osun: An ji karar harbin bindiga a wurin tattara sakamako, an kasa karasawa wurin

A yayin da hukumar zabe mai kanta ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Osun bayan jama’a sun kamala kada kuri’un su, an ji karar harbe-harben bindiga a cibiyaar tattara sakamako dake Oke Obun Ila. Yanzu haka babu halin shiga cikin cibiyar, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

A baya Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar komai ya kankama a farfajiyan sanar da sakamon zaben gwamnan jihar Osun da aka gabatar a yau Asabar, 22 ga watan Satumba. 2018.

Da alamun an kammala zabe a dukkan kananan hukumomi dake jihar Osun zuwa yanzu sabanin Ola Oluwa: Town Hall II. Ward 10. Unit 005 inda har misalin karfe shida na yamma ana cigaba da zabe sakamakon rashin isowar kayan zabe wajen har karfe 12 na rana.

Daga baya kuma na'urar 'Card reader' ya fara bada matsala wanda a kawo jinkiri a wannan waje.

Zaben Osun: An ji karar harbin bindiga a wurin tattara sakamako, an kasa karasawa wurin

Cibiyar tattara sakamako ta jiha
Source: Twitter

Da sanyin safiyar yau ne Legit.ng ta kawo maku wasu muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani dangane da zaben na yau, Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018.

1. ‘Yan takara 48 ne ke takarar neman maye gurbin gwamna Rauf Aregbesola mai barin gado

2. Adadin mutane 1,687,492 hukumar zabe (INEC) ta yiwa rajisatar zabe a jihar Osun

DUBA WANNAN: Zaben Osun: Abubuwa 6 da Kungiyoyin sa-ido suka bankado

3. Adadin katin zabe 1,246,915 INEC ta raba

4. Akwai mazabu 332 a jihar Osun

5. Jihar Osun na da kananan hukumomi 30 Manyan 'yan takarar gwamnan Osun

6. Hukumar INEC ta raba na’urar tantance masu kada kuri’a guda 4,700

7. Kungiyoyin sa ido na gida da ketare zasu halarci tare da kula da sahihancin zaben

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel