Abubuwa 6 da kungiyoyin sa-ido suka bankado a zaben jihar Osun

Abubuwa 6 da kungiyoyin sa-ido suka bankado a zaben jihar Osun

- Kungiyoyin sa ido daban-daban da suka halarci mazabu a fadin jihar Osun sun bayyana muhimman abubuwa da suka gano a zaben nay au, Asabar, 22 ga watan Satumba

- YIAGA, wata kungiyar sa-ido ta nahiyar Afrika (WTV) ta saki sakamakon abubuwan da ta gano dangane da zaben tun da tsakar rana

- Kungiyoyin na fitar da rahotanninsu ne bayan zagaye a mazabun da ake kada kuri’a a fadin sassan jihar

A yayinda jama’ar jihar Osun suka fita domin zaben sabon gwamnan da zai maye gurbin gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, da wa’adin mulkinsa ya zo karshe.

Kungiyoyin sa-ido na cikin gida da waje da suka halarci zaben sun fitar da wasu abubuwa 6 da suka gano tare da bankadowa yayin zagayen da suka yi mazabu daban-daban dake fadin jihar ta Osun.

1. Wata kungiyar sa-ido ta nahiyar Afrika ta bayyana cewar kasha 91% na ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) sun isa runfunan kada kuri’u dake sassan jihar daban-daban

Abubuwa 6 da kungiyoyin sa-ido suka bankado a zaben jihar Osun

Manyan 'yan takarar gwamna a zaben Osun

2. An fara kada kuri’u a kaso 94% na mazabu da misalin karfe 9:00 na safe

3. A kalla kowacce akwatun zabe na da ma’aikata 4. Kaso 90% na mazabu sun samu a kalla ma’aikaciyar INEC mace guda, yayin da kaso 60% na mazabu suka samu ma’aikata mata biyu ko fiye da haka.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Da fitilar kwai ake amfani a wurin tattara sakamakon zabe, hoto

4. Kashi 100% na mazabu sun samu jami’an hukumar tsaro

5. An yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a (Card Reader) a kaso 100% na mazabun jihar

6. Jam’iyyar APC na da wakilai a kasha 99% na mazabun jihar Osun, yayin da jam’iyyar PDP keda wakilai a kaso 98 na mazabu, sai kuma jam’iyyar SDP mai kaso 96%. Akwai kimanin wakilan jam’iyyu 7 a kowacce akwatun zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel