Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u

Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u

- APC da PDP na amfani da hotunan mutane 2 da rundunar yan sanda ta ce ta kama suna sayen kuri'u wajen yakar junansu.

- Jam'iyyun biyu sun musanya cewa jami'an na su ne, sai dai suna zargin junansu

Jim kadan bayan da rundunar yan sanda ta sanar da nasararta na cafke wasu mutane guda biyu da ta kama suna kokarin sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Osun da ya gudana a yau Asabar, jam'iyyun siyasa biyu, PDP da APC sun mayar da labarin kamar makamin yakar junansu.

Rundunar yan sanda ta dora hotunan mutanen biyu rike da kudade da buhun shinkafa, ba tare da bayyana ko jami'an wacce jami'an wacce jam'iyyar ba ne. Sai dai APC na ikirarim cewa jami'an PDP ne kasancewar an dauki hotonsu rike da buhun shinkafa mai hoton Sanata Adeleke a jiki.

Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u

Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u
Source: Twitter

Haka zalika ita ma PDP na ikirarin cewa mutanen da aka kama jami'an APC ne kasancewar an nuno su rike da makudan kudade, wadanda ta yi zargi tun a baya cewa APC za ta yi duk me yiyuwa wajen samun nasarar cin zaben gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Ana ci gaba da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Osun

Jam'iyyun biyu dai sun mayar da hotunan wadannan mutane kamar makaman yakar junansu, hoto daya, zargi daya, banbancin jam'iyya da kuma banbancin kudi da buhun shinkafa. Suna amfani da shafukansu na Twitter don caccakar junansu.

Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u

Osun 2018: Rikici ya barke tsakanin APC da PDP akan jami'an da aka kama suna sayen kuri'u
Source: Twitter

A dai Legit.ng ta ruwaito maku yadda rundunar yan sanda ta sake cafke wani jami'i dauke da kudade, da ya ke sayen kuri'un mutane a zaben. Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.

Haka zalika mun ruwaito maku cewa wasu da ake kyautata zaton yan ta'adda ne sun kai farmaki a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Orolu, a jihar Osun, inda suka tarwatsa mutanen da ke kada kuri'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel