Ribadu ya shiga cikin sahun manema takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

Ribadu ya shiga cikin sahun manema takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar ta Adamawa.

A ranar yau ta Asabar tsohon shugaban hukumar ya bayyana kudirin tsayawa takarar inda zai kalubalanci gwamnan jihar, Muhammadu Bindow, yayin neman tikitin takara na jam'iyyar APC.

Legit.ng ta fahimci cewa, bayyanar wannan kudiri na Mallam Ribadu ba zai yiwa gwamna Bindow dadi ba sakamakon aniyar neman tazarcen kujerarsa da ya kudirta a karkashin jam'iyyar APC inda zai fafata a zaben 2019.

Ribadu ya shiga cikin sahun manema takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

Ribadu ya shiga cikin sahun manema takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa
Source: Depositphotos

A yayin ganawarsa da jiga-jigan jam'iyyar a hedikwatar ta dake birnin Yola na jihar Adamawa, Ribadu ya bayyana cewa, kokari gami da hobbasan Gwamna Bindow kan karagar mulki ta jihar bai kai ga tsammanin da aka sanya a gare sa ba.

KARANTA KUMA: 2019: Abdulsalami ya yi gargadi kan rugurgujewar Najeriya

A sanadiyar hakan ya sanya tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana kudirinsa sakamakon muhimmiyar bukata da za ta kawo sauyi da sabon salo ta fuskar shugabanci na jam'iyyar a jihar.

Kazalika Mallam Ribadu ya nemi shugabannin jam'iyyar akan su bayar da dama ta zube ban kwarya yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar domin gamsar da kowane manemin takara ta fuskar adalci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel