2019: Abdulsalami ya yi gargadi kan rugurgujewar Najeriya

2019: Abdulsalami ya yi gargadi kan rugurgujewar Najeriya

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsali Abubakar, ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa makiyi kuma babban abokin gaba ga duk wanda ya yi yunkurin dakile kwararar romon dimokuradiyya a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa zai dawwama cikin kasancewa abokin gaba ga duk wanda ya yi yunkurin kawo nakasun ci gaban dimokuradiyya ko kuma jefa kasar nan cikin rudani da rikici a yayin zaben 2019.

Janar Abdulsalami ya bayyana hakan ne yayin halartar wata lacca da aka gudanar a jami'ar Ibadan ta jihar Oyo kan hadin gwiwar samuwa da tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

2019: Abdulsalami ya yi gargadi kan rugurgujewar Najeriya

2019: Abdulsalami ya yi gargadi kan rugurgujewar Najeriya
Source: UGC

Tsohon shugaban kasar ya kuma gargadi 'yan siyasar kasar nan akan shigo da wani sabon lamari da zai kawo tangarda a yayin zaben 2019.

A cewarsa, Najeriya ba za ta taba kasancewa kasar da muke muradi ba muddin ba mu hada kai wuri guda ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma sanya soyuwar juna a zukatan mu.

KARANTA KUMA: Yadda 'Kwayoyin Cutar Zika ke warkar da Cutar Daji ta 'Kwakwalwa

Ya kuma jaddada bukatar al'ummar Najeriya akan su mayar da hankali da kulawa wajen kawo karshen rikita-rikitar dake kawo zagon kasa da barazana ga ci gaban kasar nan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, tsohon shugaban kasar ya kuma shawarci daliban jami'ar ta Ibadan akan su karaucewa duk wata hanya da ba ta dace ba ta yin amfani da su domin cimma manufar siyasa a yayin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel