Zaben 2019: Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yake ganin ya cancanci tikitin takarar PDP

Zaben 2019: Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yake ganin ya cancanci tikitin takarar PDP

- Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yafi Kwankwaso, Saraki cancanta

- Yace da shi aka kafa jam'iyyar ta PDP

- Ya kuma ce shi bai taba fita daga jam'iyyar ba

Daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya dake neman tikitin takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya roki 'yan jam'iyyar da su yi masa halacci musamman ma shi da bai taba fita daga jam'iyyar ba.

Zaben 2019: Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yake ganin ya cancanci tikitin takarar PDP

Zaben 2019: Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yake ganin ya cancanci tikitin takarar PDP
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Zaman sulhu: An tashi baran-baram a tsakanin yan takarar PDP

Alhaji Sule yayi wannan rokon ne a lokacin da yake zantawa da jiga-jigan jam'iyyar da za su gudanar da zaben fitar da gwani na jihar Nasarawa a cigaba da yawon zumuncin da yake yi.

Legit.ng ta samu cewa Sule da yake jawabi a wajen taron, ya kara da cewa yana daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar ta PDP a shekarar 1998 kuma tun lokacin har yanzu bai taba fita ba.

Jam'iyyar ta PDP dai yanzu haka mutane da dama sun nuna sha'awar su ta neman tikitin ta domin shiga zabukan gama gari da za'a gudanar a shekarar 2019 da suka soma sayar da fom din.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana goyon bayan takarar shugancin kasar Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal keyi.

Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya din a ranar Asabar a gidan sa dake a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel