Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa

Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa

- Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa

- Yace dole ne su su tsage gaskiya komin dacin ta

- Ya bayar da kuma misali da ministan wasanni

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta dake ke kudu maso kudancin Najeriya Cif Ayiri Emami ya yi ikirarin cewa dayawa daga cikin wadanda ke zagaye da Shugaba Buhari sune ke dagula masa lissafi.

Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa

Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa
Source: Facebook

KU KARANTA: Hukumar kididdiga ta fadi yawan bashin da ake bin Najeriya

Cif Ayiri yace musamman ma ministocin gwamnatin Shugaba Buhari kwata-kwata basu don suka cigaban sa kuma a lokutta da dama sukan zamo tamkar 'yan hana ruwa gudu a sha'anin tafiyar da gwamnatin ta sa.

Legit.ng ta samu cewa Cif Ayiri ya fadi hakan ne a lokacin dake zantawa da wakilin majiyar mu inda har ma ya bayar da misalin cikin ministocin Shugaba Buhari na wasanni da matasa watau Barista Solomon Dalung inda yace yana yakar gwamnatin ne ma a kai kai ce.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana goyon bayan takarar shugancin kasar Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal keyi.

Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya din a ranar Asabar a gidan sa dake a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel