Zaben 2019: Babangida ya goyi bayan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

Zaben 2019: Babangida ya goyi bayan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

- Babangida ya goyi bayan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

- Dan takarar dai shine Aminu Waziri Tambuwal

- Yace yanayin tsarin sa yana burge shi

Tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana goyon bayan takarar shugancin kasar Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal keyi.

Zaben 2019: Babangida ya goyi bayan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

Zaben 2019: Babangida ya goyi bayan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a PDP
Source: Twitter

KU KARANTA: Ambaliyan ruwa ya ci hanyar kauyen su Jonathan

Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya din a ranar Asabar a gidan sa dake a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Legit.ng ta samu cewa a lokacin ziyarar gwamnan na Sokoto, an tsinkayi tsohon shugaban kasar yana ta zunduma masa albarka tare da yaba masa musamman ma a wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Haka zalika ya yaba wa matashin kuma gogaggen dan siyasar akan kokarin da yake yi wajen tabbatar da hadin kan Najeriya ba tare da la'akari da addinance ko kabilanci ba.

A wani labarin kuma, Hukumar kididdiga ta kasa watau National Bureau of Statistics, (NBS) a turance a cikin wani sabon daftarin rahoton kididdiga ta fadi yawan kudaden da ake bin kasar Najeriya da yanzu haka ke karkashin kulawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Alkaluman da hukumar ta fitar dai sun bayyana cewa kawo yanzu ana bin Najeriya kudaden da suka kai dalar Amurka biliyan 22.08 daga kasashen waje yayin da kuma ake bin kasar Naira triliyan 3.48 daga cikin gida Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel