Ofishin kididdiga na kasa zai kashe biliyoyi kan kididdigar yawan talakawa

Ofishin kididdiga na kasa zai kashe biliyoyi kan kididdigar yawan talakawa

- Mamaki kan yadda agajin kudin zai tafi kan kididdigar talakawa ba magance talaucin ba

- Kudin zai zo ne daga bankin duniya har dala miliyan hudu

- Za'a shekara ana wannan aiki, kuma za'a dauki ma'aikata a fadin kasar nan

Ofishin kididdiga na kasa zai kashe biliyoyi kan kididdigar yawan talakawa

Ofishin kididdiga na kasa zai kashe biliyoyi kan kididdigar yawan talakawa
Source: Instagram

Agajin baban bakin duniya a wannan karon, ga hukumar kididdiga ta kasa, zai zo ne ta fannin dauko duk wasu bayanai na jama'a da suka shafi aikin gona, neman arziki, da yaduwar talauci, da ma duba yadda ayyukan gwamnati ke sauya rayuwa musamman a karkara.

Aikin dai na binciken, zai dauki tsawon shekara daya, kuma ya kamata a dinga yi duk shekaru biyar, zai kuma ci $3.5m, kusan biliyan daya kenan na nairori.

DUBA WANNAN: Za'a biya malaman kaduna hakkokinsu

Sabbin bayanan, zasu baiwa gwamnati damar fahimtar yadda ayyukan gwamnati da agajin kungiyoyin kasa-da-kasa ke shafar talakawa, kuma hukumar kididdiga ta NBS ita zata aiwatar dashi daga badi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel