Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Amurka gobe Lahadi

Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Amurka gobe Lahadi

Shugaba kasa, Muhammadu Buhari zai sake tafiya kasar Amurka gobe Lahadi, 23 ga watan Satumba 2018 domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya na 73 a hedkwatan majalisar dake birnin New York.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya saki a yau Asabar inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi New York gobe Lahadi domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya UNGA37 wanda aka kaddamar ranan 18 ga watan Satumba, 2018."

Taken taron gangamin na wannan shekaran shine: "Ganin cewa majalisar dinkin duniya ta amfani mutane gaba daya'. The highpoint of President Buhari’s participation will be his address on Tuesday to the General Assembly on the opening day of the General Debate.

Babban abinda Buhari zai yi a Amurka shine jawabinsa da zai gabatar ga taron gangamin ranan Talata, 25 ga watan Satumba 2018 inda zai jaddada matakin da Najeiya take dauke wajen samar da zaman lafiya da tsaro."

Kana ana sa ran zai bukaci taimakon kasashen duniya wajen yaki da rashawa, dawo da kudaden sata da kuma yaki da ta'addanci."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel