Osun 2018: Muna fatan za a kirga kuri'un mutane ba tare da magudi ba - EU

Osun 2018: Muna fatan za a kirga kuri'un mutane ba tare da magudi ba - EU

- Kungiyar hadakar kasahen turai EU ta ce tana fatan za a kirga kuri'un da aka kada a zaben Osun ba tare da aringizo ba

- EU na fatan wannan zaben na jihar Osun zai zama kamar fitilar da zata haska babba zaben 2019

- Ta bayyana masu kad'a kuri'a a jihar Osun a matsayin mutane masu dattako da sanin ya kamata

Jakadan kungiyar hadakar kasashen turai EU, Mr. Ketil Karlsen, ya ce yana fatan hukumar INEC za ta kirga sakamakon zaben da jama'a suka kad'a ba tare da aringizo ko magudi, don samar da sahihin sakamakon zaben jihar Osun da aka kammala a wasu sassa na jihar.

Karlsen, wanda ya ke daya daga cikin masu saka idanu akan gudanar da zaben, ya shaidawa manema labarai a Irabiji jihar Osun, cewa EU na fatan wannan zaben na jihar Osun zai zama kamar fitilar da zata haska babba zaben 2019.

Ya bayyana masu kad'a kuri'a a jihar Osun a matsayin mutane masu dattako da sanin ya kamata, tare da kuma jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bisa yadda ta tsara gudanar da zaben cikin salo na zamani.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Adeleke ya samu nasara a rumfar zabensa

Osun 2018: Muna fatan za a kirga kuri'un mutane ba tare da magudi ba - EU

Osun 2018: Muna fatan za a kirga kuri'un mutane ba tare da magudi ba - EU
Source: Twitter

Ya ce: "Tun safe muke nan muna sa ido kan yadda ake gudanar da zaben; mu 55 ne a tawagarmu, masu sanya ido 28 daga kasashen turai, kuma bisa ga yadda bubuwa ke gudana, komai yana tafiya lafiya kamar yadda ake so.

"Haka zalika jami'an tsaro sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin zaben ya gudana cikin lumana ba tare da tashin hankula ba. Wannan shi ake kira demokaradiya, wacce ke nuna makomar al'umma da kasarsu. Muna fatan wannan zaben ya zama fitilar haska babban zaben 2019."

Duk da cewa Karlsen ya ce ba zai iya yanke hukunci akan sakamakon karshe na ingancin zabe ba, har sai zuwa lokacin da aka kammala, ya jinjinawa mutane bisa nuna dattako yayin da suka hau layi don jefa kuri'arsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel