An yi tururuwa wajen Zaben Gwamnan jihar Osun cikin tsaro mai tsanani

An yi tururuwa wajen Zaben Gwamnan jihar Osun cikin tsaro mai tsanani

Da sanadin shafin jaridar Leadership mun samu rahoton cewa, al'ummar jihar Osun sun yi tururuwa zuwa wajen zaben gwamnan jihar da a halin yanzu ake ci gaba gudanarwa a ranar yau ta Asabar domin kada kuri'unsu na zabe.

Binciken rahotanni da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, al'umma sun yi tururuwa gami dandazo na zuwa kada kuri'unsu yayin zaben gwamnan jihar Osun dake ci gaba da wakana yau din nan.

Ziyarar da manema labarai suka kai wasu yankunan mazabu uku na jihar ta tabbatar da cewa, akwai tsaro mai tsananin gaske yayida jami'ai na hukumomin tsaro daban-daban ke faman sintiri da kai komo na jiran tsammani ko ta kwana.

An yi tururuwa wajen Zaben Gwamnan jihar Osun cikin tsaro mai tsanani

An yi tururuwa wajen Zaben Gwamnan jihar Osun cikin tsaro mai tsanani
Source: UGC

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa, akwai adadin wuraren kada kuri'u 3,010 cikin mazabu uku masu dauke da kananan hukumomi 30 dake fadin jihar.

KARANTA KUMA: Jerin tsaffin Gwamnoni 15 dake rike da Kujeru a Majalisar dattawa

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai jam'iyyu 48 dake fafatawa a yayin wannan zabe na gwamnan jihar, inda dan takarar jam'iyyar APC, Gboyega Oyetola, Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP da kuma Iyola Omisore na jam'iyyar SDP ke kan gaba.

Legit.ng ta fahimci cewa, an fara gudanar da wannan zabe tun misalin karfe 8.00 na safiyar yau ta Asabar, inda wasu masu kada kuri'un musamman a babban birnin jihar na Osogbo suka yi sammakon fita tun karfe 6.00 na Asubahin yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel