Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

- Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

- Yanzu dai mutanen garin suna shan wahala

- Sun roki Shugaba Buhari da ya taimaka masu

Hanyar garin Otuoke zuwa Onuebum dake a cikin karamar hukumar mulki ta Ogbia, jihar Bayelsa dake zaman hanya daya tilo mafi sauki ta zuwa kauyen su tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan watau Otuoke ta cika da ruwa sakamakon ambaliya.

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

KU KARANTA: Wani lauya ya maka Buhari kotu

Majiyar mu ta kamfanin dillacin labaru ta ruwaito mana cewa yanzu haka dai masu bin hanyar dole ta sa sun canza hanya ya zuwa bin wata doguwar domin kaucewa ambaliyar.

Legit.ng ta samu cewa wani ma'aikacin jami'ar tarayya ta garin Otuoke watau Federal University Otuoke, FUO, mai suna Mista Clever Ogbodi ya shaidawa majiyar tamu cewa yanzu suna matukar shan wahala sakamakon toshewar hanyar.

Mista Clever ya kara da cewa su da ke bin hanyar a da sukan biya Naira 250 ne kacal kafin su je jami'ar amma yanzu saboda bin sabuwar hanyar Naira 400 ne suke biya don haka ne ma ya roki gwamnati da ta taimaka ta gyara masu hanyar.

A wani labarin kuma, Dakarun sojin Najeriya tuni sun soma aikin zuke tafkunan wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Jos ta kudu dake a jihar Filato a cigaba da zurfafa binciken neman gawar dan uwan su da ya bace a kwanan baya.

A baya dai mun kawo maku labarin cewa wani babban jami'in rundunar sojin ta kasa mai suna Manjo Janar Idris Alkali ya bata a kan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel