Osun 2018: Jami'an tsaro sun sake cafke jami'in PDP yana sayen kuri'u don a zabi Adeleke

Osun 2018: Jami'an tsaro sun sake cafke jami'in PDP yana sayen kuri'u don a zabi Adeleke

- Wani jami'in jam'iyyar PDP ya shiga hannun jami'an tsaro bayan da aka kamashi yana kokarin sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Osun

- Rahotanni sun bayyana cewa an kama jami'in ne yana kokarin rabawa masu kad'a kuri'u kudi don su zabi dan takarar jam'iyar Sanata Adeleke

- Zuwa yanzu jami'an PDP hudu ne aka kama da laifin sayen kuri'u

Labarin da Legit.ng ta ke samu yanzu na cewa jami'an tsaro sun sake cafke wani jami'in PDP a kokarin da ya ke yi na sayen kuri'un ta hanyar biyan jama'a kudi don su zabi dan takarar jam'iyyar, Sanata Ademola Adeleke.

Jami'in PDP da hukumar tsaro ta sake cafkewa yana sayen kuri'u a zaben Osun 2018

Jami'in PDP da hukumar tsaro ta sake cafkewa yana sayen kuri'u a zaben Osun 2018
Source: Facebook

A wani labarin makamancin wannan:

Rundunar yan sanda sun samu nasarar cafke wasu jami'an jam'iyyar PDP guda biyu a kokarin da suke yi na sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Osun da ake kan gudanarwa yanzu. Wannan na daga cikin yunkurin da hukumar INEC ta ke yi na gudanar da sahihin zabe.

Bisa wannan rahoto da rundunar ta samu, kodinetan tsaro a zaben, Joshak Habila, wanda shine mataimakin Sifeta Janar na rundunar yan sanda DIG, ya bayar da umurnin cafke su da zaran an gansu.

KARANTA WANNAN: Osun 2018: Rundunar yan sanda ta cafke wasu jami'an PDP guda 2 a kokarin da suke yi na sayen kuri'u

Jami'an PDP da aka kama suna sayen kuri'u a zaben Osun

Jami'an PDP da aka kama suna sayen kuri'u a zaben Osun
Source: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Zaben Osun: Shin Adeleke na PDP zai iya kayar da Oyetola na APC? | Legit.ng TV

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel