Osun 2018: Rundunar yan sanda ta cafke wasu jami'an PDP guda 2 a kokarin da suke yi na sayen kuri'u

Osun 2018: Rundunar yan sanda ta cafke wasu jami'an PDP guda 2 a kokarin da suke yi na sayen kuri'u

- Rundunar yan sanda sun samu nasarar cafke wasu jami'an jam'iyyar PDP guda biyu a kokarin da suke yi na sayen kuri'u

- Mataimakin Sifeta Janar na rundunar yan sanda DIG, ne ya bayar da umurnin cafke su da zaran an gansu

- Itama jam'iyyar PDP ta zargi APC da siyen kuri'u a wasu rumfunan zabe na jiahr inda ta ce ana rabawa masu kada kuri'a N10,000 ko N20,000

Rundunar yan sanda sun samu nasarar cafke wasu jami'an jam'iyyar PDP guda biyu a kokarin da suke yi na sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Osun da ake kan gudanarwa yanzu. Wannan na daga cikin yunkurin da hukumar INEC ta ke yi na gudanar da sahihin zabe.

Bisa wannan rahoto da rundunar ta samu, kodinetan tsaro a zaben, Joshak Habila, wanda shine mataimakin Sifeta Janar na rundunar yan sanda DIG, ya bayar da umurnin cafke su da zaran an gansu.

Habila wanda ya bayyana cewa bai kamata ace ana ganin jami'an suna yawo daga akwati zuwa akwati ba, kasancewar ya saba da dokar zabe ta 2011, ya kuma ce rundunar ba zata dagawa duk wanda ta kama yana yawace yawace a rumfunan zabe ba, ma damar baida babbar hujja.

KARANTA WANNAN: Adeleke: Jam'iyyun hamayya na tsoron a gudanar da sahihin zabe a Osun, sun san zan yi nasara

Osun 2018: Rundunar yan sanda ta cafke wasu jami'an PDP guda 2 a kokarin da suke yi na sayen kuri'u

Osun 2018: Rundunar yan sanda ta cafke wasu jami'an PDP guda 2 a kokarin da suke yi na sayen kuri'u
Source: Twitter

Bisa rahotannin da ke yawo, jam'iyyar PDP na siyen kuri'un ne ta hanyar bayar da kudi ko kuma shinkafa da dai sauran kayan abinci a cikin buhuna dauke da hoton dan takarar gwamnan jihar karkashin PDP, Sanata Ademola Adeleke.

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa itama jam'iyyar PDP ta zargi APC da siyen kuri'u a wasu rumfunan zabe na jiahr inda ta ce ana rabawa masu kada kuri'a N10,000 ko N20,000, wanda kuma rundunar yan sanda ta basu tabbacin daukar mataki akan hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel