Assha: An kama APC tana sayen kuri'u a zaben Osun

Assha: An kama APC tana sayen kuri'u a zaben Osun

Sahara Reporters ta tabbatar da cewa wasu wakilan jam'iyyar APC na sayan kuri'un masu zabe a yankin dan takarar gwamna na jam'iyyar, Isiaka Gboyega Oyetola.

Ana kiran masu kada kuri'ar zuwa wani gida ne da ke da fostocin Oyetola a kofar gidan kasancewar gidan na kusa da rumfar kada kuri'an, an gano cewa wakilan jam'iyyar APC na cikin gidan kuma rabawa mutane N2,000 kafin su tafi su jefa kuri'unsu.

Sai dai wakilan na APC sun ankare cewa wakilan Sahara Reporters na daukansu bidiyo hakan yasa su ka umurci masu kada kuri'an su tafi su dawo bayan sa'a guda domin karbar kudaden na su.

Bidiyon ya nuna yadda masu zabe su kayi layi suna jiran a fara raba musu kudin da daya daga cikin wakilan APC na kidiya kudade a hannunsa.

Ga bidiyon yadda abin ya kasance a kasa.

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel