Adeleke: Jam'iyyun hamayya na tsoron a gudanar da sahihin zabe a Osun, sun san zan yi nasara

Adeleke: Jam'iyyun hamayya na tsoron a gudanar da sahihin zabe a Osun, sun san zan yi nasara

- Ademola Adeleke, ya ce ma damar aka gudanar da sahihin zabe to babu makawa shine zai samu nasarar zama gwamnan jihar Osun

- Ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kada kuri'arsa

- Ya ce gaba daya yan takarar gwamnan suna jin tsoronsa shi yasa ma suka kulla masa tuggun da ba su samu nasara ba

Ademola Adeleke, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da ke kan gudana, ya bayyana cewa ma damar aka gudanar da sahihin zabe to babu makawa shine zai samu nasarar zama gwamnan jihar.

Ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kada kuri'arsa.

Da ya ke maida martani kan makircin da ake kulla masa, ya karyata jita jitar da ake yadawa akansa, ya na mai cewa an bullo da wannan makircin ne kawai don bata masa sunan a idon al'umma da kuma fitar da shi daga takara ta karfin tsiya.

Ya bayyana cewa ya tsallake dukkanin matakan cancantar tsayawa takara don a zabe shi.

KARANTA WANNAN: Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

OsunDecides2018: Adeleke a lokacin da ya ke kada kuri'arsa

OsunDecides2018: Adeleke a lokacin da ya ke kada kuri'arsa
Source: Original

Ya ce: "Ina da yakinin cewa zan samu nasara a wannan zaben. Duk wani makirci da aka jingina shi akaina karya ne. Suna kokari ne kawai suga cewa ban tsaya takara a zaben ba. Amma na san cewa na cancanta a zabe ni, kuma jama'ata za su zabeni.

"Gaba dayansu suna tsoro na, saboda sun san idan na tsaya wannan takarar kuma aka gudanar da sahihin zabe to babu makawa nine zan samu nasara akansu.

"Da ikon Allah, za a gudanar da sahihin zabe, kuma zan samu nasara," a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel