Zaben Osun: Abunda zan yi idan na fadi zabe – Sanata Adeleke

Zaben Osun: Abunda zan yi idan na fadi zabe – Sanata Adeleke

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sanata Ademola Adeleke ya bayyana cewa zai taya abokin adawarsa murna idan har ya fadi zaben gwamnan jihar Osun.

A wani hira da manema labarai a ranar Asabar, 22 ga watan Satumba, bayan ya jefa kuri’arsa a mazabarsa dake Ede ta arewa, sanatan ya bayyana cewa akwai alamun cewa shine zai lashe zaben, inda ya kara da cewa zai tura sakon taya murna ga duk wanda ya yi nasara idan har shi bai ci ba.

Ya kuma nuna gamsuwa da tsarin zuwa yanzu, inda ya bayyana cewa kayayyaki sun isa wurin da wuri.

Zaben Osun: Abunda zan yi idan na fadi zabe – Sanata Adeleke

Zaben Osun: Abunda zan yi idan na fadi zabe – Sanata Adeleke
Source: Original

Da Legit.ng ta tambaye shi akan yiwwar nasararsa, dan takaran yace zai yi nasara idan har zaben ya kasance na gaskiya da amana.

KU KARANTA KUMA: Ministan Buhari da bai yi NYSC ba ya kare kansa

A halin da ake ciki mun ji cewa wata tsohuwar kakakin majalisar wakilai, Patricia Etteh ta bayyana cewa tana da yakini kan cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce zata yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa a yau Asabar, 22 ga watan Satumba.

Etteh wacce tayi Magana da jaridar The Nation daga gidanta na Ikire, tace jam’yyar ta shirya ma zaben dari bisa dari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel