Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

Dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar APC, Adegboyega Oyetola ya isa akwatin da ke mazabarsa, inda ya hau layi aka tantance shi tare da kad'a kuri'arsa, a zaben gwamnan jihar da ke kan gudana yanzu.

Oyetola ya isa akwati na 6 na gundumar sa ta I, a karamar hukumar Irabaji da misalin karfe 10:05 na safe inda ya samu rakiyar matarsa. Kai tsaye ya hau layi don tantance shi, daga bisani kuma ya kada kuri'arsa.

Kafin tsayawa takarsa, Oyetola shine shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar mai ci a yanzu, karkashin gwamna Rauf Aregbesola, wanda hasashe ke ganin cewa shine zai samu nasarar lashe zaben a karawarsa da dantakarar gwamnan karkashin PDP Sanata Adeleke.

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa
Source: Original

Duk da cewa akwai jam'iyyun siyasa 48 da ke harin kujerar gwamnan jihar da ke gudana a yau asabar 22 ga watan Satumba, jam'iyyu 5 ne daga cikin su ake ganin zasu ja daga fiye da sauran, inda zasu fuskanci masu kad'a kuri'a 1,246,915 a jihar.

Daga cikinsu akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar, Fatai Akinbade, daga jam'iyyar ADC; sakataren gwamnatin jihar wanda ya sauka kwanan nan, Mashood Adeoti na jam'iyyar ADP; dan takarar APC, Adegboyega Oyetola; da kuma Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP, tare da tsohon Sanata, Iyiola Omisore na jam'iyyar SDP.

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa
Source: Original

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa

Zaben Osun 2018: Dan takarar gwamnan jihar karkashin APC ya kad'a kuri'arsa
Source: Original

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel