Ministan Buhari da bai yi NYSC ba ya kare kansa

Ministan Buhari da bai yi NYSC ba ya kare kansa

- Ministan sadarwa, Adebayo Shittu ya kare kansa daga korafe-korafen da akeyi saboda ba shi da takardar NYSC

- Shittu ya amsa cewa bashi da takardan NYSC amma tun farko bai yi karyar yana da ita ba saboda haka bai aikata laifi ba

- Ministan ya ce aikin da ya yi a matsayinsa na dan majalisa jiha ta fi yiwa kasa muhimmanci kuma har yanzu kasa ya ke yiwa hidima

A jiya ne, MInistan Sadarawa na kasa, Barrista Adebayo Shittu ya yi karrin haske kan rahoton da wasu kafafen yadda labarai suka wallafa na cewa bashi da takardan shedan yiwa kasa hidima wato NYSC.

Wani ministan Buhari da baiyi NYSC ba ya kare kansa

Wani ministan Buhari da baiyi NYSC ba ya kare kansa
Source: Depositphotos

A hirar da ya yi da manema labarai bayan an tantance shi a matsayin dan takarar gwamna a Abuja, ya amince bashi da takardan NYSC sai dai ya ce lamarinsa ya sha ban-ban da na tsohuwar Ministan Kudi, Kemi Adeosun saboda bai kawo takardan bogi ba.

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Ministan ya ce a ra'ayinsa, yana ganin Hidimar da ya yiwa jiharsa a lokacin da aka zabe shi a matsayin dan majalisar jiha ta fi muhimmanci, ya kuma kara da cewa rashin yiwa kasa hidimar ba laifi bane muddin mutum bai yi karyar cewa ya yi ba.

"Nigerian Tribune ta wallafa cewa na kammala jami'a a 1979 amma gaskiya itace na bar jami'a a 1978 na kuma kammala makarantar koyan aikin lauya a 1979 kuma dokar kasa ta ce dole ne duk wanda ya yi takarar zabe kuma ya yi nasara ya tafi ofishinsa ya yi aiki kuma nayi aikin shekaru 4 a majalisar jiha.

"A gani na hidimar da na yiwa jiha ta a majalisa ta fi hidimar kasa muhimmanci kuma ko a yanzu ma kasa ta nake yiwa hidima," inji Shittu.

Ministan ya ce hankalinsa kwance ya ke kuma idan akwai wani da ke da hujjar da tafi tasa sai ya bayyana inda ya saba dokar kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel