Yadda 'Kwayoyin Cutar Zika ke warkar da Cutar Daji ta 'Kwakwalwa

Yadda 'Kwayoyin Cutar Zika ke warkar da Cutar Daji ta 'Kwakwalwa

Wani sabon bincike na masana kiwon lafiya da jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, akwai yiwuwar kwayoyin cutar Zika na iya magance ɓarna gami da rugurguza tasirin cutar Kansa ta cikin kwakwalwa da aka fi sani da cutar Daji.

An wallafa sakamakon wannan binciken cikin wata mujalla ta Jami'ar Texas dake kasar Amurka a ranar Talatar da ta gabata, bayan tsawon shekaru da masana kiwon lafiyar suka shafe na gudanar da bincike kan gano ainihin hanyar da kwakwalwa ke kamuwa da kwayoyin cutar Zika.

Kazalika kwararrun na kiwon lafiya sun yi bincike kan lahanin da kwayoyin cutar Zika ke yiwa kwakwalwar Bil Adama, inda a cutar Glioblastoma multiforme (GBM) ta yiwa duk wata cutar Daji ta kwakwalwa fintinkau ta fuskar lahani da duk wanda ya kamu da ita bai ko kara shekaru biyu a doron kasa.

Yadda 'Kwayoyin Cutar Zika ke warkar da Cutar Daji ta 'Kwakwalwa

Yadda 'Kwayoyin Cutar Zika ke warkar da Cutar Daji ta 'Kwakwalwa
Source: Depositphotos

Sai dai sabon binciken da masana kimiyar suka gudanar ya bayyana cewa, akwai kyakkyawan zato dangane da yadda za a yi amfani da kwayoyin cutar Zika wajen kashe kwayoyin cutar ta GBM ba tare da wani lahani ga dan Adam ba.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamnan jihar Osun ya zo karshe, an fara kidayar 'Kur'iu

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, illa gami da lahanin cutar Zika ta shahara a kasar nan na ta Najeriya yayin da annobar cutar ta barke a shekarar 2015 da ta gabata.

Jagoran wannan bincike, Dakta Shi Peiyong, shine ya bayar da tabbacin hakan tare da cewa, binciken da suka gudanar ya bayyana yiwuwar yadda za a yi amfani da kwayoyin cutar Zika wajen magance mafi lahanin cutar Daji ta kwakwalwa ba tare da yiwa kwakwalwar lahani ko janyo sauyin tunani ko hankali ga mai ita ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel