2019: Dalilai 5 da suka sa Tinubuya ya janye goyon bayansa ga Ambode

2019: Dalilai 5 da suka sa Tinubuya ya janye goyon bayansa ga Ambode

- A shekarar 2015 ne Akinwumi Ambode ya lashe zaben gwamnan jihar Legas karkashin jam’iyyar APC bayan ya kayar da ragowar ‘yan takara da suka hada da Jimi Agbaje

- Kafin zabensa a matsayin gwamna, Ambode ys kasance ma’aikacin gwamnatin jihar Legas na tsawon shekaru 27

- A yayin day a rage saura wasu ‘yan watanni zuwa babban zaben shekarar 2019, jagoran jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya juyawa gwamna Ambode baya

A yayin da takarar gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, ke karar fuskantar barazanar tangarda saboda rashin samun goyon bayan jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, Legit.ng ta bankado wasu daliliai 5 da suka kawo wannan Baraka tsakanin mutanen biyu.

1. Tsarin gwamnbatin Ambode a kan tsaftace Legas

Garin Legas na daga cikin kazaman birane dake Najeriya saboda yawan jama’a da take da shi. A baya, kafin zuwan Ambode, tsohon gwamna jihar Legas, Babatunde Fashola, ya kirkiro tare da bullo da wasu hanyoyi na tsaftace garin Legas, musamman yaki da zubar da shara da yin bahaya ko ina. Sai dai Tinubu na ganin cewar wasu Ambode ya gaza cigaba da aiwatar da irin aikin da Fashola ya yi domin tsaftace garin Leagas.

2. Girman kan Ambode

Biyayyara Ambode ga Tinubu da kuma wasu ‘yan siyasa c eta saka suka yanke shawarar bashi takarar gwamna a shekarar 2014. Sai dai rahotanni sun bayyana cewar Ambode ya daina ‘yan siyasar da suka kafa shi girma tare da yin mulki ba tare da tuntubar su ba.

2019: Dalilai 5 da suka sa Tinubuya ya janye goyon bayansa ga Ambode

Tinubuya da Ambode
Source: Depositphotos

3. Rashin tsari a siyasance

Akwai babbar alamar ayar tambaya a kan way eke juya akalar siyasar jihar Legas tsakanin gwamna Ambode da tsohon gwamna Fashola. Rashin yin tafiya da ‘yan siyasar dake kasa ya kara kawo nakasu ga tafiyar siyasar Ambode a jihar Legas.

4. Yin burus da Tinubu a tafiyar da harkokin gwamnati

Rahotanni sun bankado cewar Tinubu ya dade da haushin Ambode a ransa, ya tsaya ne kawai jiran lokaci ya yi da zai hukunta shi. Hakan ne ya saka duk wani yunkurin lallaba Tinubu ya yafewa Ambode ke neman cin tura.

DUBA WANNAN: 2019: Buhari ya kafa kwamitin yakin neman zabensa

5. Sha’awar Tinubu na bawa sabbin ‘yan siyasa dama

Yanzu dai haka Tinubu na goyon bayan tsohon kwamishinan jihar Legas kuma mai masa biyayya, Sanwo-Olu, a matsayin mutumin da zai maye gurbin Ambode.

Sanwa-Olu na daga cikin yaran Tinubu da suka nuna sha’war su ta yin gadar kujerar mulki daga wurin Fashola amma sai Tinubu ya nemi su hakura domin a tsayar da Ambode.

Ganin Ambode ya bashi kunya ne ya saka Tinubu yanzu ke ganin gara a bawa sabuwar fuska dama bisa tunanin zai cigaba da aiyukan raya Legas kamar yadda ke cikin tsarin jihar na zama katafaren birni a Afrika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel