Kwankwaso ya bayyana adadin mogoya bayansa da ke jihar Kano

Kwankwaso ya bayyana adadin mogoya bayansa da ke jihar Kano

- Sanata Kwankwaso ya ce adadin magoya bayansa da ke jihar Kano masu rajitsa a jam'iyya sun kai 2.5 miliyan

- Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar kamfe a Legas domin ganawa da deleget din jam'iyyar

- Sanatan mai wakiltan Kano ta Tsakiya ya ce Kano da Legas ne jihohin da su kafi tasiri wajen zaben shugaban kasa saboda yawan al'ummarsu

Jagoran tafiyar Kwankwasiya kuma daya daga masu neman tikitin takarar shugabancin kasa karkashin jma'iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa adadin 'yan Kwankwasiya masu rajistan jam'iyya a Kano sun kai 2.5 miliyan.

Ya ce idan akayi la'akari da adadin magoya bayansa a jihar, za a iya ganin cewa yana da muhimmiyar rawa da zai taka a babban zaben 2019 mai zuwa.

Kwankwaso ya bayyana adadin 'yan moya bayansa da ke jihar Kano

Kwankwaso ya bayyana adadin 'yan moya bayansa da ke jihar Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

Kwankwaso ya yi wannan maganar ne a jihar Legas yayin da ya ke ganawa da deleget gabanin zaben fitar da gwani na PDP, inda ya fada musu cewa magoya bayansa na karuwa daga dukkan sassan Najeriya.

Sanatan ya tunatar da su cewa shine ya samu kuri'u mafi yawa yayin zaben kujerar Sanata da akayi a Kano a shekarar 2015 inda ya samu kuri'u 760,000 a yankin Kano ta Tsakiya.

Ya kuma ce Legas da Kano suna kamanceceniya ta fuskar yawan al'umma, ya kara da cewa jihohin biyu ne za su zama sanadin duk wanda zai lashe zaben duk da cewa ya yi imanin PDP ce za ta lashe zaben.

Kwankwaso ya shaidawa deleget din cewa ya umurci dubban magoya bayansa da ke Legas suyi rajista da PDP kuma ya bukaci shugabanin jam'iyyar su karbe su hanu biyu-biyu domin tabbatar da ganin jam'iyyar tayi nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel