2019: EFCC ta sha alwashin hukunta masu siye da siyar da kuri’u

2019: EFCC ta sha alwashin hukunta masu siye da siyar da kuri’u

Yayinda ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2019, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jaddada yunkurinta na kawar da rashawa a shirin zabe don tabbatar da cewa yan siyasa basu siye yancin al’umma ba.

A yayin da za’a gudanar da zaben gwamna a jihar Osun a karshen makon nan, hukumar ta tura jami’anta don yin bincike domin kawar da duk wani yunkuri da za kai ga siyar da kuri’u da kuma tursasawa na kudi da ya addabi harkar zaben kasar.

2019: EFCC ta sha alwashin hukunta masu siye da siyar da kuri’u

2019: EFCC ta sha alwashin hukunta masu siye da siyar da kuri’u
Source: Depositphotos

Musamman, hukumar ta bayyana shirinta na zuba ido akan yanda jam’iyyun siyasa zasu kashe kudade a yakin neman takara, yayinda take kira ga yan takara da su bi tsarin dokar zabe kan kashe-kashen kudade yayin yakin neman zabe kamar yanda idan yan takara suka ki bin doka, za’a dauke su tamkar masu hannu a rashawa kuma hukumar zata hukunta su kamar yanda doka ta tanadar.

KU KARANTA KUMA: Zan iya kayar da Buhari kuma nayi sa’ar kasancewa dan Kano - Kwankwaso

Wannan mataki da hukumar ta dauka,kamar yanda shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya nuna, ta kasance daga cikin yunkuri na ganin hukumar EFCC ta hada hannu da sauran hukumomin doka a kasar don gabatar da hukuncin dokar zabe wanda ke haramta jami’an siyasa dsa masu takara yin amfani da kudi wajen tursasawa al’umma yayinda da ake gudsanar da yakin neman zabe da kuma inda ake gudanar da zabe a ranar zabe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel