'Karin bayani kan babban Jami'in rundunar Sojin kasa da ya ɓace a garin Jos

'Karin bayani kan babban Jami'in rundunar Sojin kasa da ya ɓace a garin Jos

Wani sabon rahoto da ya bayyana da sanadin hukumar rundunar sojin kasa ta Najeriya ya bayyana cewa, an samu karin bayanai dangane da wani babban jami'in sojin, Manjo Janar Idris Alkali, da ya ɓace a garin Jos na jihar Filato.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tuni rundunar sojin kasa ta fara aikin zuke Gulabe dake garuruwa da kuma kauyukan karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a yayin ci gaba da zurfafa bincike na neman gawar dan uwansu da ya danna layar zana a kwanan baya.

Rahotanni da suka bayyana kwanaki kadan da suka gabata sun ruwaito cewa, babban dakarun sojin ya bace ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja.

'Karin bayani kan babban Jami'in rundunar Sojin kasa da ya ɓace a garin Jos

'Karin bayani kan babban Jami'in rundunar Sojin kasa da ya ɓace a garin Jos
Source: Depositphotos

Sai dai a yayin da dakarun soji tare da hadin gwiwar wani kamfanin gine-gine na kasar China suke aikin zuke Gulaben garuruwa da kauyukan, wasu Mata sun aiwatar a zanga-zangar lumana na nuna rashin amincewa da wannan lamari domin a cewar su ruwan na amfanar su.

KARANTA KUMA: Kwamitin Shugaban Kasa ya bayyana abinda ya haddasa Girgizar 'Kasa a garin Abuja

Lamarin ya sanya nauyin wannan aiki ya rataya a wuyan dakarun sojin kadai a yayin da kamfanin ya janye kayansa na aiki domin neman zaman lafiya da kuma gujewa barazana.

Ko shakka ba bu binciken dakarun sojin da suke zargin an jefa Motar abokin aikin su cikin wani Gulbi, ya tabbatar da yiwuwar akwai wasu Motocin na daban dake cikinsa, inda a halin yanzu sun tsamo wata babbar Mota kirar Hummer mai cin Mutane 18 a cikin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel