Najeriya na bukatar shugaban kasar da zai mutunta doka – Tambuwal

Najeriya na bukatar shugaban kasar da zai mutunta doka – Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yace Najeriya na bukatar shugaban kasar da zai mutunta doka sannan kuma yayi duba ga sake fasalin lamuran kasar.

Ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 21 ga watan Satumba lokacin da ya gana da shugabannin Peoples Democratic Party (PDP), a jihar Ekiti gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Yace ya yanke shawarar takarar kujeran shugaban kasa a 2019 bayan lura da cewar gwamnatin Buhar ta gaza ta fannin shugabanci.

Tambuwal ya kuma bada tabbacin cewa zai goyi bayan fafatukar sake fasalin Najeriya har idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019.

Najeriya na bukatar shugaban kasar da zai mutunta doka – Tambuwal

Najeriya na bukatar shugaban kasar da zai mutunta doka – Tambuwal
Source: Depositphotos

Ya zargi gwamnatin APC da nuna bangaranci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sabon rikici ya balle a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara, hakan yayi sanadiyar samun rabuwar kai tsakanin gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da mataimakinsa, Ibrahim Wakkala.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Shia ta Labanon, Hizbulla, tace wai tanadi manyan makamai masu linzami

Hakan na zuwa ne bayan da wasu daga cikin masu son jam'iyyar ta tsayar da su takara suka yi zargin cewa gwamnan ya dade da zabar wanda yake so ya gaje shi, kuma yake kokarin turasasa shi a kan al'umma, hakan ya sa mataimakin gwamnan tare da wasu 'yan takarar guda bakwai suka nuna turjiya akan wannan yunkuri nasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel