Zaben 2019: Dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa - Tambuwal

Zaben 2019: Dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa - Tambuwal

- Tambuwal ya sha alwashin goyon bayan samar da wasu jihohi don sake fasalin kasar idan har aka zabe shi a 2019

- Ya ce ya yanke hukunci tsayawa takarar shugaban kasa don magance manyan kura kuran da gwamnatin Buhari ta tafka

- Ya ce suna sane da makircin APC na ci gaba da kasancewa akan mulki

Gwamna jihar Sokoto, wanda kuma ya ke son jam'iyyar PDP ta tsaida shi a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Hon. Aminu Tambuwal, a ranar Juma'a ya sha alwashin goyon bayan samar da wasu jihohi don sake fasalin kasar idan har aka zabe shi a 2019.

Tambuwal, wanda ya dau wannan alkawari a Ado Ekiti a wani taro da jami'an da ke kada kuri'a a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP, ya kara da cewa fadar shugaban kasa har kullum itace ake kallo a matsayin alamar cikar kasa.

Ya bayyana cewa ya yanke wannan hukunci na tsayawa takarar shugaban kasa biyo bayan sha'awarsa ta kishinsa na magance manyan kura kuran da gwamnatin Buhari ta tafka musamman a bangaren tabarbarewar shugabanci da gazawa wajen yiwa jama'a ayyukan raya kasa.

KARANTA WANNAN: Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere

Zaben 2019: Dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa - Tambuwal

Zaben 2019: Dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa - Tambuwal
Source: Facebook

Ya sha alwashin gudanar da nagartaccen shugabanci cikin kwarewa da zai samar da hadin kan Nigeria da kuma sake fasalin kasar ta yadda kasashen duniya za su rinka kallon kasar da idon daraja.

Gwamnan jihar Sokoton ya bukaci mambobin jam'iyyar PDP da su kasance masu nuna kishi da kwarin guiwa duk da irin cin mutuncin da gwamnatin APC take yiwa wasu daga cikin shuwagabannin su.

Ya ce: "Babban burin duk wani dan Nigeria shine ya zabi shugaban kasa mai kishin Nigeria, wanda baya nuna banbancin akida ko addini. Muna sane da irin makirce makircen da gwamnatin yanzu ke yi na kasancewa akan mulki. Wannan ne ma ya sa suke cin mutuncin shuwagabannin PDP kamar irinsu gwamna Ayodele Fayose.

KARANTA WANNAN: Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook

"Ya zama wajibi a gareku, ku baiwa dan jam'iyyar PDP wanda ya yarda da sake fasalin kasar tutar shugabanci, wanda yasan matsaloli da hanyoyi magance su. Wanda ya yi aiki a kashin kansa daga Maiduguri zuwa Legas, daga Fatakwal zuwa Sokoto, sannan daga Gabas zuwa Arewa.

"A matsayina na tsohon mataimakin mai horas da bangaren marasa rinjaye, daga baya na zama shugaban marasa rinjaye, har na dawo na zama kakakin majalisar wakilai ta tarayya, na tabbata ina da cikakkiyar masaniya kan hanyoyin da za a yiwa kasar garanbawul, don haka ina tunanin na kai kololuwar da jama'a za su bani dama don shugabantar su," a cewar Tambuwal.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Zaben jihar Osun 2018: Nawa ne zai isa mutum ya zabi dan takara? | Legit.ng TV

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel