2019: Buhari na da bangaranci, ya matsu ya ga kan shi akan mulki - Tambuwal

2019: Buhari na da bangaranci, ya matsu ya ga kan shi akan mulki - Tambuwal

- Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, ya bada tabbacin cewa zai goyi bayan fafatukar sake fasalin Najeriya

- Tambuwal ya sha alwashin daidaita al'amuran kasar idan ya lashe zabe a 2019

- Yace gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza, tare da nuna tarin bangaranci

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bada tabbacin cewa zai goyi bayan fafatukar sake fasalin Najeriya har idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019.

Mista Tambuwal, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, ya dauki alkawarin ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma’a, 21 ga watan Satumba yayinda yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar.

2019: Buhari na da bangaranci, ya matsu ya ga kan shi akan mulki - Tambuwal

2019: Buhari na da bangaranci, ya matsu ya ga kan shi akan mulki - Tambuwal
Source: Facebook

A kwanakin baya ne dan takaran ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP inda yake da niyar tsyawa takarar kujeran shugabancin kasar.

Yace kamfen dinsa ba zai fifita wutar kabilanci ba sannan kuma zai gujema bangarenci kamar yadda ake “fuskanta a gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari”.

KU KARANTA KUMA: Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

Yace ya yanke shawarar takarar kujeran shugaban kasa a 2019 bayan lura da cewar gwamnatin Buhar ta gaza ta fannin shugabanci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel