Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere

Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere

- Rundunar yan sanda ta ce ta cafke wanda ake zargi da kashe Farfesa Simon Ocheme Apakwu

- Rundunar ta cafke Oluche ne a garin Jos, jihar Filato, a lokacin da ya ke kokarin badda kamannin motar don sayar da ita

- An gano gawar Farfesa Apakwu a gidansa, a ranar Juma'a, 14 ga watan Satumba, 2018

Rundunar yan sanda ta jihar Gombe ta ce ta samu nasarar cafke wanda ake zargi da kashe Farfesa Simon Ocheme Apakwu, wani malami da ke koyarwa a jami'ar gwamnatin tarayya ta Kashere, da ke jihar Gombe.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr Shina Tairu Olukolu, ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da ya gabatar da wanda ake zargin, mai suna Simon Oluche, mai shekaru 25, ranar Juma'a, a harabar shelkwatar rundunar.

Ya ce wanda ake zargin, wanda ya kasance direban mamacin, ya kashe marigayi Farfesa Apakwu tare da guduwa da motarsa, wasu kayayyaki mallakin mamacin da kuma makudan kudaden da ba a bayyana adadinsu ba.

KARANTA WANNAN: Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook

Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere

Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere
Source: Depositphotos

Olukolu ya ce rundunar ta cafke Oluche ne a ranar 18 ga watan Satumba a garin Jos, jihar Filato, a lokacin da ya ke kokarin badda kamannin motar don sayar da ita, wacce ya sace bayan kashe farfesan mai shekaru 65.

Rundunar yan sanda ta ce wanda ake zargin ya samu bayanin cewa jami'ar Kashere ta baiwa farfesan wasu kudade, don haka ne ya gayyato abokansa, wadanda suka taimaka masa wajen gudanar da danyen aikin.

Kwamishinan rundunar ya ce jami'an da ke bincike kan lamarin sun bi sahun wanda ake zargin don cafke shi jim kadan bayan da ya aikata kisan.

Legit.ng ta tattara bayanai kan cewar an gano gawar Farfesa Apakwu a gidansa, a ranar Juma'a, 14 ga watan Satumba, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Nigeria na bukatar Naira tiriliyan 4 don kawo karshen talauci | Legit.ng TV

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel