Kuma dai: An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

Kuma dai: An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

- An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

- Zaman ya gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar

Mun samu labarin cewa an tashi ba'a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kuma dai: An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

Kuma dai: An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP
Source: Twitter

KU KARANTA: Wasu 'yan agaji sun yi hatsari akan hanyar su ta zuwa Kaduna daga Jos

Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam'iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa masu neman tikitin takarar jam'iyyar da suka samu halartar zaman sun hada da Sanata Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da Sanata David Mark.

Sauran sun hada da tsaffin Gwamnoni kamar sun Jona Jang; Ahmed Makarfi; Rabiu Kwankwaso da dai sauran su.

A wani labarin kuma, Wasu alkaluma da muka samu daga babban ofishin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) dake a garin Abuja, babban birnin tarayya na nuni ne da cewa akalla mutane 1,973 yanzu haka ke takarar kujerun majalisun tarayya a jam'iyyar.

Idan aka kara rarraba wadannan alkaluman, za kuma a ga cewar akalla mutane 386 ne suka sayi fom din neman takarar kujerar dan majalisar dattawa yayin da kuma mutane 1,587 suka sayi fom din yin takarar majalisar wakilai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel