Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Shugaba Buhari

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Shugaba Buhari

- Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Shugaba Buhari

- Yace masoyan nashi makiyan demokradiyya ne

Daya daga cikin manyan malaman addinan kirista a kasar nan kuma shugaban rukunin majami'un Mount Zion Faith Global Liberation Ministry Inc.( a.k.a. By Fire By Fire) da ke a garin Nnewi, jihar Anambra mai suna Bishop Abraham Udeh ya yi kaca-kaca da masoya Muhammadu Buhari.

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Shugaba Buhari

Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani Lauya ya maka Buhari da Buratai kotu

Bishop din wanda a jiya ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa dukkan masu son Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarce to lallai shi babban makiyin demokradiyya ne.

Legit.ng ta samu cewa ya kuma kara da cewa kusan dukkan shika-shikai da sharuddan demkradiyya shugaban kasar da gwamnatin sa sun sa kafa sun shure su a lokuta da dama a lokacin mulkin su.

Haka zalika babban bishop din ya bayar da misali da yadda bangaren zartarwa ya rika yiwa bangaren majalisar shigar hanci da kudundune tare da kasalandan lamarin da ya ce sam bai dace ba.

A wani labarin kuma, Wani lauya dake ikirarin rajin kare hakkin bil'adama mai suna Mista Oleka Udenze dake zama a garin Abuja ya maka shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da wasu mukarraban gwamnatin sa game da shirin Atisayen rawar mesa na uku watau Operation Python Dance 3 a turance.

Shirin dai na 'Operation Python Dance' na zaman wani mataki da sojojin Najeriya suka dauka a watannin baya da nufin kakkabe dukkan wasu hatsabiban tsageru a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke son ballewa daga Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel