Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

- Mai taimakawa shugaba Buhari a fanin sabuwar kafar yada labarai, Bashir Ahmad ya lissafa wasu gwamnonin APC da basu da hamayya a jihohinsu

- Gwamnonin da ya lisaffa sun hada da Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, El-Rufai na jihar Kaduna da Aminu Masari na jihar Katsina

- Ya kuma ce shugaba Muhammadu Buhari shima ba shi da wata hamayya a halin yanzu

Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai kuma jagoran Cibiyar Tallata Buhari, Bashir Ahmad ya ce akwai gwamnoni 10 na jam'iyyar APC da ke neman zarcewa kan mulkin kuma basu da wata kwakwarar hamayya kamar yadda Buhari shima bashi da ita.

Wasu daga cikin gwamnonin da ya lissafa wadanda ba su da abokan hammaya zaben fitar da gwamni a jihohinsu sun hada Dr Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Gwamna Bello Aminu Masari na jihar Katsina da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Bashir Ahmad ya yi wannan jawabin ne ta shafinsa na dandalin sada zumunta ta Twitter a yau Juma'a 21 ga watan Satumban 2018 misalin karfe 11.41 na safe.

A dai jiya ne 'yan masu neman takarar kujeru na gwamna da majalisar tarayya a karkashin jam'iyyar APC suka garzaya babban birnin tarayya Abuja domin a tantance su kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar da za'ayi nan ba da dadewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel