Zaben 2019: Yawan 'yan takarar kujerun majalisun tarayya 469 a jam'iyyar APC

Zaben 2019: Yawan 'yan takarar kujerun majalisun tarayya 469 a jam'iyyar APC

- An bayyana yawan 'yan takarar kujerun majalisun tarayya 469 a jam'iyyar APC

- Ance akalla mutane 1,973 yanzu haka ne ke takarar kujerun

- Tuni dai aka rantsar da kwamitocin da za su tantance

Wasu alkaluma da muka samu daga babban ofishin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) dake a garin Abuja, babban birnin tarayya na nuni ne da cewa akalla mutane 1,973 yanzu haka ke takarar kujerun majalisun tarayya a jam'iyyar.

Zaben 2019: Yawan 'yan takarar kujerun majalisun tarayya 469 a jam'iyyar APC

Zaben 2019: Yawan 'yan takarar kujerun majalisun tarayya 469 a jam'iyyar APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Cikin shekara 2 zan gyara Najeriya - David Mark

Idan aka kara rarraba wadannan alkaluman, za kuma a ga cewar akalla mutane 386 ne suka sayi fom din neman takarar kujerar dan majalisar dattawa yayin da kuma mutane 1,587 suka sayi fom din yin takarar majalisar wakilai.

Legit.ng dai ta samu cewa tuni dai shugaban jam'iyyar ta APC na kasa baki daya, Kwamared Adams Oshiomhole ya rantsar da kwamitocin da za su tantance dukkan 'yan takarar kamar dai yadda doka jam'iyyar ta tanadar.

Wasu daga cikin shugabannin kwamitocin da za suyi aikin na tantancewar dai sun hada da Farfesa Oserheimen Osunbor, Cif Timipre Sylva, Sanata Ahmad Sani Yerima, Sanata Ken Nnamani, Sharon Ikeazor, Sanata. Bukar Abba Ibrahim, Sanata Olorunnimbe Mamora da dai sauran su.

A wani labarin kuma, Wani lauya dake ikirarin rajin kare hakkin bil'adama mai suna Mista Oleka Udenze dake zama a garin Abuja ya maka shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da wasu mukarraban gwamnatin sa game da shirin Atisayen rawar mesa na uku watau Operation Python Dance 3 a turance.

Shirin dai na 'Operation Python Dance' na zaman wani mataki da sojojin Najeriya suka dauka a watannin baya da nufin kakkabe dukkan wasu hatsabiban tsageru a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke son ballewa daga Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel