Cakwakiya kan takarar gwamna: Buhari da Gwamnoni na iya takawa Bola Tinumbu birki

Cakwakiya kan takarar gwamna: Buhari da Gwamnoni na iya takawa Bola Tinumbu birki

- Akwai yuwuwar rabuwar kawuna tsakanin shugabancin kasa da gwamnonin APC

- Ya janye goyon bayan Ambode ne saboda wani tsohon kwamishina

- An matsawa shugaban jam'iyyar da ya canza tunani

Cakwakiya kan takarar gwamna: Buhari da Gwamnoni na iya takawa Bola Tinumbu birki

Cakwakiya kan takarar gwamna: Buhari da Gwamnoni na iya takawa Bola Tinumbu birki
Source: Twitter

Tunanin wanda zai zamo gwamnan jihar Legas na gaba zai iya kawo rabuwar kawuna tsakanin shugabancin kasa, gwamnonin APC da kuma shugaban jam'iyyar APC ta kasa Bola Ahmed Tinubu da magoya bayan shi.

Tinubu ya janye goyon bayan Ambode domin sake darewa kujerar shugabancin jihar Legas sabo wani tsohon kwamishinan kasuwanci da masana'antu, Mista Babajide Sanwo-Olu.

An matsawa shugaban jam'iyyar da ya canza ra'ayi.

Gwamnonin sun shawarci shugaban kasa da kada ya bar Tinubu ya guji Ambode wanda suke kira da 'Gwamnan Gwamnoni'.

DUBA WANNAN: Yayi mata wayau a bandakin makaranta, yanzu kotu zata daure shi

A ranar talata ne gurin zagayen kamfen na dan jam'iyyar APC na jihar Osun, Buhari, wasu gwamnoni da shuwagabannin jam'iyyar suka roki Tinubu da ya ba Ambode dama.

Majiyar mai karfi daga jam'iyyar tace Buhari na ganin cewa hakan zai iya zama barazana ga kuri'ar shi ta jihar Legas.

Shugaban ya damu da yankin kudu maso gabas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel