Gwamnati za ta fara kididdige yawan talakawan Najeriya

Gwamnati za ta fara kididdige yawan talakawan Najeriya

Shugaban Hukumar Kididdiga ta kasa, Yemi Kale, ya bayyana cewa hukumar za ta fara aiki kididdige adadin talakawan da ke fadin kasar nan daga ranar 27 ga Satumba.

Shirin kamar yadda Kale ya bayyana da bakin sa, zai gano gejin da kudaden shiga da kuma karfi korashin karfin samun wadatar abinci da nauyin iya ciyar da kai na kowane matalauci.

Ya bayyana hakan ne a wani taron kara wa juna ilmi da hukumar ta shirya a Keffi, jihar Nasarawa.

Wannan aikin inji shi, zai dauki shekara daya cur yana gudana.

Gwamnati za ta fara kididdige yawan talakawan Najeriya

Gwamnati za ta fara kididdige yawan talakawan Najeriya

Ya ce an fito da shirin ne domin a san takamaiman adadin matalautan Najeriya, ta yadda za a samu daidaito a wurin kididdiga da gamsasshen lisafi ingantacce da gwamnati za ta rika amfani da shi.

Ya nuna yakinin cewa hakan zai sa gwamnatin tarayya a kan hanyar samun nasarar ayyukan raya al’umma da ta sa a gaba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Sambo zai tantance Saraki, Atiku, Tambuwal da sauransu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba ta bayyana cewa ta ware kudi na mussaman domin tallafawa manoman shinkafa don ganin an karya farashin shinkafa yar gida.

Ministan gona da raya karkara, Cif Audu Ogbeh yace bankin noma da ma’aikatar ne zasu kula da kudin inda ya kara da cewa gwamnati tayi wannan karamcin ne domin tabbatar da cewar shinkafa yar gida tayi araha sannan kuma tafi shinkafa yar waje farin jini a kasuwa.

Yayi Magana ne a lokacin wani taro na kungiyar manoman shinkafar Najeriya Rice Farmers Association of Nigeria (RIFAN) da masu sarrafa shinkafa a ofishinsa dake Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel