Da dumi-dumi: Gwamnan mulkin soji na farko a jihar Kwara ya rasu

Da dumi-dumi: Gwamnan mulkin soji na farko a jihar Kwara ya rasu

Mun samu daga Daily Trust cewa gwamnan mulkin soji na farko a jihar Kwara, Brigadier Janar David Bamigboye ya rasu a jihar Legas bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

An samu labarin rasuwar ne daga bakin wani dan uwan mamacin wanda ya rasu yana da shekaru 78 a duniya. Ya kuma ce za'a sanar da ranar da za'ayi jana'izar mariagayi Bamigboye nan gaba.

Brigadier Janar David Bamigboye ya mulki jihar Kwara ne daga 1967 zuwa 1975 bayan an kafa jihar daga tsohuwar Yankin Arewa lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon mai murabus.

Da dumi-dumi: Gwamnan mulkin soji na farko a jihar Kwara ya rasu

Da dumi-dumi: Gwamnan mulkin soji na farko a jihar Kwara ya rasu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

David Bamigboye dan kabilar Igbomina ne daga Omu Aran da ke karamar hukumar Irepodun da ke jihar Kwara. An haife shi ne a 1940 kuma bayan ya sauka daga mulki ya mikawa maraigayi Ibrahim Taiwo shi kuma ya mikawa Hassan Katsina.

A shekarar 1968, ya kirkiri Ma'aikatan Ilimi ta jihar Kwara wadda ke da sashi na musamman domin kula da bawa daliban makarantu tallafi.

A 1971 ya sanar da niyyarsa ta kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kwara wato Kwara State Polytechnic wadda aka kafa a 1972.

A shekarar 1977, gwamnati ta kwace wasu daga cikin kadarorinsa da ke Ilorin kuma sai da aka kwashe shekaru 26 kafin aka mayar masa a Mayun 2003.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel