Kotun Najeriya ta daure wani dan kasuwa tsawon shekaru 140 a Kurkuku saboda laifin daya aikata

Kotun Najeriya ta daure wani dan kasuwa tsawon shekaru 140 a Kurkuku saboda laifin daya aikata

Wata babbar kotun Najeriya a karkashin mai sharu Muhammed Idris ta yanke ma wani dan kasuwa hukuncin zaman gidan kaso na tsawo shekaru dari da arba’in akan wasu laifuka daya tafka, inji rahoton jaridar sahara reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta shigar da karar dan kasuwan mai suna Jones Biyere inda take tuhumarsa da aikata laifuka guda goma sha uku.

KU KARANTA: Wata budurwa yar bindiga ta bindige mutane 3 har lahira, ta kashe kanta

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne a ranar Alhams 20 ga watan Satumba, inda yace hukuncin zaman gidan kaso na shekaru goma goma akan tuhume tuhume guda goma sha daya, sai kuma hukuncin shekaru goma sha biyar biyar da tuhuma ta 12 da ta 13.

Sai dai Alkalin yace Jones zai zauna na tsawon shekaru sha biyar ne kacal saboda zai gudanar da duka horon ne a tare,; “Bangaren masu kara sun gamsar da kotu akan tuhume tuhumen da suke yi ma wanda ake kara.

“Haka zalika shaidun da masu kara ta kawo gaban Kotu sun tabbatar da wanda ake karar ya tafka laifin da ake tuhumarsa, kuma shima wanda ake karar ya amsa laifinsa, sai dai ya kasa baiwa kotu kwakkwaran dalilinsa na aikata wannan laifi.

“Tunda lauyan wanda ake kara ya nemi a yi masa sassauci saboda dan kasuwa ne, kuma mai kula da iyali, sa’annan wannan ne karonsa na farko daya tafka laifi, amma fay a bata mana lokaci a wannan shari’ar saboda halayyarsa.” Inji Alkali.

Tun a shekarar 2006 aka shari’ar Jones akan laifin shirya takardar cirar kudi ta bogi da kuma fitar da wadannan takardu zuwa kasashen waje, EFCC tace Jones yaso yayi amfani da kamfanin UPS ne wajen fitar da takardun.

A cewar EFCC laifin ya saba ma sashi na 3(2)a, 6(2)b da 6(1)a na kundin kananan laifuka na Najeriya na shekarar 1990, kuma hukuncinsa na nan a sassi na 3 da 3(b) na laifukan shirya kudade bogi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel